Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta girmama batutuwan sulhun da suka tattauna a tsakaninsu da kungiyar ASUU da sauran kungiyoyin manyan makarantu a kasar nan.
Shugaban Kungiyar ta NLC Ayuba Wabba shi ne ya yi wannan kiran ta cikin sakon sa na bikin Easter na Bana ga ma’aikata da kuma al’ummar kasar nan, mai taken “Fatan Da Baya Taba Mutuwa” da aka gudanar jiya a Abuja.
Ya ce miliyoyin daliban jami’oin kasar nan musamman masu karatu a manyan makarantun gwamnati, sun gudanar da bukukuwan su na Easter a gida sabanin yadda suka saba a makarantun su.
Ya kara da cewa “muna bukatar mutunta yarjejeniyoyin hadin gwiwa da suka rattaba hannu da kungiyoyin malaman jami’a da sauran sassan ta.”
Wabba ya kuma bayyana cewa har yanzu ma’aikata da dama a Najeriya ba su ci gajiyar mafi karancin albashi ba kusan shekaru hudu bayan da aka sanya hannu kan dokar, yana mai cewa jihar Cross River da Taraba da Zamfara ne jihohin da har yanzu ba su fara aiwatar da mafi karancin albashin ba.
Shugaban na NLC ya kuma ce suma ‘yan fansho ba su tsira ba la’akhari da yadda yawancin su ake hana su kudaden alawus-alawus da kuma kudaden fansho da suke bin gwamnati.
Ya ce, abin takaicin shi ne, yayin da ma’aikata ke ci gaba da gudanar da ayyukansu, wasu lokutan kuma ba a biyan su albashi, ga tsadar rayuwa na ci gaba da ta’azara, lamarin daya durkusar da abubuwa a gefe guda kuma Naira ta ci gaba da fuskantar faduwar daraja.
A cewarsa, Kungiyar na jinjinawa ma’aikatan Najeriya, bisa nuna halin rashin gajiyawa tare da bukatar su da su ci gaba da yarda cewa sabuwar Najeriya mai ma’aikata da zaman lafiya tana nan tafe nan gaba.
“A wannan biki na Ista, muna rokon ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da su hadu su rokawa kasa mafita a wajen mahaliccinmu”.
Wabba ya kuma ce yawan kashe-kashen da aka yi a jihar Filato, da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, da sauran su, wata yar manuniya ce da karara ke nuna gazawar Gwamnati a harkokin tsaro.
Ya ce kungiyar ta bukaci gwamnati ta tabbatar da dawo da duk wadanda aka sace nan bada jimawa ba.











































