A yau laraba ne aka kammala taron tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ASUU.
Taron wanda ya gudana a hedikwatar ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya da ke Abuja, ya dauki tsawon sa’o’i 8, amma an dage zaman har zuwa ranar litinin mako mai zuwa domin ci gaba da tattaunawa.
Da yake zantawa da manema labarai a karshen taron, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, ya ce daga cikin batutuwa takwas da aka gabatar a kan teburin tattaunawa, an samu fahimtar juna a bangarori hudu na bukatun ASUU.
Akan tsarin biyan albashi na UTAS da ASUU ta samar domin maye gurbin IPPIS, Dokta Ngige ya bayyana cewa za a kafa wani kwamitin kwararru na hadin gwiwa da zai gwada da kuma warware duk wani abu da ke kewaye da sabon tsarin.
Sai dai kuma a kan batun asusun farfado da jami’o’in, ministan ya dage cewa tattaunawa a duk fadin yankin na bukatar shigar da ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa kafin a yanke shawara ta hakika.
Duk da cewa shugaban kungiyar ASUU na kasa Farfesa Emmanuel Osodeke ya ki cewa komai a karshen taron, tun da farko ya ce gwamnatin tarayya ta gaza gudanar da taron sa ido kan aiwatar da ayyuka na yau da kullum kamar yadda aka amince.
Tun da farko dai a wajen bude taron, ASUU ta dage kan cewa ba za a yi wani yunkuri ba har sai an biya musu bukatunsu.













































