TikTok ta musanta takaita amfani da manhajarta a Arewacin Najeriya

TikTok

Shafin sada zumunta na TikTok ya ce bai takaita amfani da manhajarsa a yankunan Arewacin Najeriya ba.

Shugabar Sashen Hulɗa da Jama’a ta TikTok a yankin Afirka kudu da hamadar Sahara, Keagile Makgoba, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, yayin da ake samun rahotannin matsalolin shiga manhajar.

Makgoba ta ce TikTok na tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samar da mafita kan matsalolin shiga manhajar da aka ruwaito.

“Za mu iya tabbatar da cewa ba TikTok ne ya sanya wannan takunkumi ba,” in ji ta.

Makgoba ta ce kamfanin na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa al’ummomin da ke amfani da manhajarsa suna samun damar shiga.

A baya, kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa wata gamayyar ƙungiyoyin fararen hula ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan rahotannin katsewar ayyukan manhajar a wasu sassan Arewacin Najeriya.

Ƙungiyoyin sun ce masu amfani da TikTok a jihohin Kaduna, Kebbi, Kano da Sakkwato sun fuskanci matsalolin ɗora bidiyo, kallon abubuwan da aka wallafa da kuma ɗora sabbin abubuwa tun ranar 14 ga Satumba.

Sun buƙaci hukumomin da abin ya shafa da kamfanonin sadarwa da su binciki musabbabin matsalar, tare da bayyana wa jama’a ko umarni daga wani ɓangare ne ko kuma matsalar fasaha ta haddasa hakan.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here