Yanzu-Yanzu: Tsohon jarumin fina-finai Olu Jacobs, ya rasu

Olu Jacobs 750x430

Tsohon jarumin fina-finan a Najeriya kuma mai shirya fina-finai, Oludotun Baiyewu Jacobs, wanda aka fi sani da Olu Jacobs, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Dan marigayin, Olusoji Jacobs, ne ya sanar da rasuwarsa a wani sako da ya wallafa a shafin Instagram a ranar Laraba, 16 ga Satumban 2026.

A cikin sanarwar, iyalin mamacin sun kwantata tsohon jarumin da “Zakin Lufodo”, sannan sun bukaci masu rubutun ra’ayoyi a shafukan yanar gizo (bloggers) da masu fada a ji a shafukan sada zumunta da su girmama sirrinsu na iyali a wannan lokaci.

“Cike da godiya ga Allah bisa rayuwa mai kyau da kuma fadi-tashi da aka yi, muke sanar da rasuwar miji, uba, kaka, kuma kawunmu abin kauna. Zakin Lufodo.

Oludotun Baiyewun Jacobs (MFR)

Muna kira ga dukkan ma’abota shafukan yanar gizo da masu fada a ji a shafukan sada zumunta da su mutunta sirrin iyalinmu a wannan lokaci.”

Jacobs na daya daga cikin fitattun tsofaffin jaruman Najeriya kuma an san shi sosai saboda gudunmawar da ya bayar a fannin wasan kwaikwayo na dabe, talabijin da kuma fina-finai.

Ya yi karatu a makarantar wasan kwaikwayo ta Royal Academy of Dramatic Art da ke kasar Ingila, kuma ya fara harkar wasan kwaikwayo ne a Birtaniya, inda ya yi aiki da gidajen wasan kwaikwayo daban-daban, ya kuma fito a shirye-shiryen talabijin na Birtaniya da fina-finan kasa da kasa.

Bayan dawowarsa Najeriya, ya zama babban jigo a masana’antar fina-finai ta kasa, kuma ana daukarsa a matsayin daya daga cikin iyaye na gaba-gaba a masana’antar Nollywood.

Jacobs ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na rukunin babban jarumi a gasar Africa Movie Academy Award a shekarar 2007. Ya kuma karbi kyautar girmamawa ta Industry Merit Award a taron Africa Magic Viewers’ Choice Awards na shekarar 2013, da kuma kyautar sadaukar da kai ga aiki ta “AMAA Lifetime Achievement Award” a shekarar 2016.

An karrama shi da lambar yabon kasa ta Member of the Order of the Federal Republic (MFR) a shekarar 2011.

Jacobs yana auren tsohuwar jaruma fim Joke Silva.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here