Yanzu-Yanzu: Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci ta Kano ya yi murabus

Saidu Yahaya

Shugaban Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Saidu Yahaya, ya ajiye aikinsa.

SolaceBase ta rawaito cewa Yahaya ya mika takardar murabus dinsa a ranar Talata.

Murabus din nasa ya biyo bayan matsin lamba daga Gwamnatin Jihar Kano kan abin da ake zargin gazawarsa wajen sauke nauyin da ake tsammani daga gare shi.

An nada shi shugaban PCACC a watan Agustan 2025, bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da nadin nasa na shekaru biyar.

Idan za a iya tunawa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya soki shugaban a bainar jama’a a kwanakin baya kan abin da ya bayyana a matsayin rashin nuna kwazo a matsayinsa na shugaban hukumar yaki da cin hanci.

Ana sa ran Sakataren Shari’a na hukumar, Hafsat Kutama, za ta karbi ragamar shugabancin hukumar a matsayin mukaddashiya daga yau Laraba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here