Hajiya Sutura Shehu Shagari, mai ɗakin tsohon shugaban ƙasa na farko a tsarin Dimokuraɗiyya a Najeriya, Alhaji Shehu Shagari, ta rasu tana da shekara 89.
A wata sanarwa da jagora a dangin Shagari, Kyaftin Muhammad Bala Shagari (mai ritaya) ya fitar a ranar Litinin, ya tabbatar da cewa Hajiya Sutura ta rasu da misalin ƙarfe uku na rana bayan ta yi fama da rashin lafiya mai tsawo.
Sanarwar ta bayyana cewa marigayiyar ta kasance mace mai ladabi da natsuwa, uwa mai tausayi da shugabanci a gida mai cike da mutunci da biyayya, wadda ta rayu cikin kamala da tausayawa.
Dangin Shagari da abokanta sun nuna alhinin rashin ta, tare da addu’ar Allah ya jikanta da rahama, inda aka ce za a sanar da cikakkun bayanai da shirye-shiryen jana’izarta a gaba.
Hajiya Sutura ita ce matar marigayi Alhaji Shehu Shagari, shugaban ƙasa na farko a tsarin dimokuraɗiyya wanda ya yi mulki daga 1979 zuwa 1983 a ƙarƙashin jam’iyyar National Party of Nigeria.
An haifi Shehu Shagari a ranar 25 ga Fabrairu, 1925, a garin Shagari da ke cikin jihar Sakkwato ta yau, kuma ya kasance malami, ma’aikacin gwamnati da kuma ɗan siyasa da ya riƙe muƙamai daban-daban a ma’aikatun tarayya kafin ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 1979.
Mulkinsa ya fi mayar da hankali kan gidaje, ilimi, noma da masana’antu ta shirin (Green Revolution), sai dai mulkinsa ya zo ƙarshe a ranar 31 ga Disamba, 1983, bayan juyin mulki da Janar Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Alhaji Shehu Shagari ya rasu a ranar 28 ga Disamba, 2018, yana da shekara 93.













































