Sama da ƴan sanda dubu 100 daga cikin dubu 371,800 na ƙasar nan suna tsaron manyan mutane – Rahoto

Police parade

Fiye da jami’an ’yan sanda 100,000 na rundunar ’yan sanda ta ƙasa ana amfani da su ne wajen tsaron ’yan siyasa da wasu manyan mutane, lamarin da ya haifar da damuwa kan yadda ake samun ƙarancin tsaro ga talakawa, kamar yadda wani sabon rahoto ya bayyana.

Rahoto daga hukumar kula da ƙasashen Turai da ƴan gudun hijira da aka wallafa a watan Nuwamba na shekarar 2025 ya bayyana cewa rundunar ’yan sanda ta ƙasa tana da kimanin jami’ai 371,800 da ke hidima ga jama’ar da suka kai kusan miliyan 236.7.

Hukumar ta ce matsalar rashin wadatattun jami’an tsaro a ƙasar ta ƙaru ne sakamakon karkatar da yawancin ’yan sanda zuwa aikin tsaron manyan mutane maimakon aikin kare al’umma da hana aikata laifuka.

Rahoton ya ƙara da cewa rashin isassun jami’ai, cin hanci, da ƙarancin kayan aiki na janyo jinkirin amsa kiran gaggawa da kuma barin wasu yankuna ba tare da jami’an tsaro ba.

Haka kuma an bayyana cewa rashin ingantattun hanyoyin ladabtarwa na sa wasu jami’an ’yan sanda ke aikata abubuwan da suka sabawa doka, kamar kama mutane ba bisa ka’ida ba, karɓar rashawa, da amfani da karfi fiye da kima.

A cewar rahoton, duk da cewa a shekarar 2023 da kuma watan Afrilu 2025 babban sifeton ’yan sanda Kayode Egbetokun ya bayar da umarni cewa a janye jami’an rundunar da ke tsaron manyan mutane, har yanzu yawancin jami’an ’yan sanda suna nan suna bawa manyan mutane tsaro.

Rahoton ya kuma ambaci shawarar hadimar shugaban ƙasa kan tsare-tsare da daidaitawa, Hadiza Bala-Usman, wadda ta ce ya kamata a daina amfani da ’yan sanda wajen kare manyan mutane, inda ta ba da shawarar cewa masu son tsaro na musamman su ɗauki masu tsaro masu zaman kansu tare da bin ka’idojin da doka ta tanada.

Ta kuma jaddada cewa wajibi ne a gyara dokar ’yan sanda domin bai wa kamfanonin tsaro masu zaman kansu damar ɗaukar nauyin wasu ayyukan da ake tilasta wa jami’an tsaro na gwamnati, domin su mai da hankali kan kare tsaron ƙasa yadda ya dace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here