Hukumar kula da masu yiwa ƙasa hidima (NYSC) ta sanar da fitar da lambobin kira na masu shirin shiga a rukunin C na shekarar 2025.
Hukumar ta tabbatar da hakan a shafinta na X a ranar Talata, inda ta bayyana cewa an fitar da lambobin bisa tsarin rajista.
Sanarwar ta bayyana cewa ƙarancin wuraren sansani a jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja ne ya sa za a iya karɓar kusan kashi 40 cikin ɗari ne kacal daga cikin waɗanda suka yi rajista domin shirin horaswa na farko.
Ga waɗanda ba su samu wurin shiga rukunin C ba, hukumar ta tabbatar musu cewa za a mayar da su cikin jerin masu shiga rukuni na gaba.
Hukumar ta kuma jaddada cewa tana da niyyar tabbatar da ingantaccen tsari na horaswa da kuma shekarar hidima mai inganci ga dukkan mahalarta.
A baya, hukumar NYSC ta buɗe rajistar ta Internet don masu shirin hidimar ƙasa na rukunin C a ranar 4 ga Nuwamba, inda aka tsara za ta ƙare a ranar 9 ga Nuwamba ga ɗaliban da suka kammala karatu a gida da kuma waɗanda suka kammala a ƙasashen waje.
Hukumar ta fitar da jadawalin inda ta bayyana cewa tantance takardun masu karatu a ƙasashen waje zai gudana daga ranar 9 zuwa 13 ga Nuwamba, yayin da aikin sashen fasaha (ICT) zai gudana daga ranar 12 zuwa 15 ga watan.
Jami’o’i masu fitar da masu hidimar ƙasa za su gudanar da buga takardun tura wurin aikin hidimar ƙasa ta internet daga ranar 16 zuwa 18 ga Nuwamba, lokacin da ake sa ran masu hidimar za su buga takardun kiran su na shiga sansani.













































