Majalisar Dattawa ta cimma matsayar gudanar da bincike kan zarge-zargen sakamakon gwajin COVID-19 na bogi da ake yi domin damfarar wasu ‘yan Najeriya a Ghana da amfani da katunan rigakafin COVID-19 na jabu a Najeriya.
Wannan ya biyo bayan wani kudiri da Sanata Ibrahim Oloriegbe (APC-Kwara) ya gabatar kuma wasu sanatoci uku ne suka mara masa baya a yayin zaman majalisar.
Taken kudurin shine “Bukatar gaggawa ta gudanar da bincike kan zargin sakamakon gwajin COVID-19 da ake amfani da shi don damfarar ‘yan Najeriya a Ghana da kuma samun katunan rigakafin COVID-19 na karya”.
Da yake gabatar da kudirin, Oloriegbe wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kiwon Lafiya ya ce kudirin ya fito ne sakamakon yawan zarge -zarge da korafe -korafe da matafiya ‘yan Najeriya ke yi a wuraren da ake killace su a Ghana.
Ya tuna cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana cutar COVID-19 a matsayin annoba a watan Fabrairu 2020.
Oloriegbe ya lura cewa, “yayin da ake cigaba da yin allurar rigakafin COVID-19 a fadin duniya, kusan kashi ɗaya cikin ɗari na mutanen duniya ne kawai suka sami cikakkiyar allurar.”
“Har yanzu biliyoyin mutane suna jiran allurar na farko, wanda babu makawa su na cikin zullumin yadda za su samu.
A cewarsa “Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shirye a duniya don ba da dama ga waɗanda aka yi wa allurar rigakafi, ko kuma za su iya tabbatar da cewa sun yi gwaji basu dauke da cutar, ‘yancin yin balaguro zuwa wasu ƙasashe, halartar manyan tarurruka, ɗaukar sabon aiki, da saurasu.
“Akwai zarge-zarge da dama dake cewa hukumomin Ghana suna cewa gwaji na nuna ‘yan Najeriya dake zuwa kasarsu na dauke da COVID-19 koda bayan gwajin da suka yi a Nijeriya ya nuna basu dauke da cutar.












































