Majalisar kolin sojin kasar nan ta amince da karin girma ga manyan jami’ai 122 zuwa mukamin Manjo Janar da Birgediya Janar.
A wata sanarwar da daraktan yada labarai na rundunar, Bigediya Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar ya ce an kara wa masu mukamin Birgediya Janar 47 girma zuwa Manjo Janar, yayin da aka karawa Kanal 75 girma zuwa mukamin Birgediya Janar.
Daga cikin jami’an da aka kara wa girma zuwa Manjo Janar akwai mai Magana da yawun Rundunar, Nwachukwu; da kuma Birgediya Janar WB Etuk, sai Kwamandan Makarantar nazarin harkokin Kudi da Gudanarwa ta Sojojin Najeriya, Birgediya janar JE Osifo.
Da sauran manyan Jami’an rundunar da aka karawa girman.
Karanta wannan: N-Power: Gwamnatin tarayya ta ci gaba da biyan basuka ga masu cin gajiyar shirin
Babban hafsan sojojin Lutanar Janar Taoreed Lagbaja ya taya sabbin manyan jami’an da iyalansu murna.
Lagbaja ya kuma bukace su da su rubanya kokarinsu domin tabbatar da kwarin gwiwar da ake da ita akan su.













































