N-Power: Gwamnatin tarayya ta ci gaba da biyan basuka ga masu cin gajiyar shirin

N power programme
N power programme

Gwamnatin tarayya ta koma biyan basuka ga masu cin gajiyar shirin N-Power.

Wadanda suka ci gajiyar dai na bin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari bashin albashin wasu watanni.

Sai dai ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu, ta ce za a ci gaba da biyan bashin da aka fara a ranar Laraba har sai an biya kowa.

Ministar ta bayyana hakan ne a shirin Siyasa na gidan talabijin na Channels ranar Alhamis.

“A yanzu haka ana ci gaba da biyan N-Power; Mun kasance a ofishi jiya har zuwa wayewar garin yau, domin ganin matasa sun samu kudaden da suke bin gwamnatin baya.

“Don haka masu cin gajiyar shirin N-Power a fadin kasar nan, na tabbata za ku iya tabbatar da cewa suna ganin kudaden ku a cikin asusu kuma wannan tsari zai ci gaba har sai an biya gaba daya kudaden da suke bi.

“Kuma ba shakka, duk wannan muna yi ne don ganin mun rage rashin aikin yi da samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya,” in ji Edu.

Karanta wannan: Festus Keyamo ya nada sabbin daraktoci na hukumomin Jiragen sama

Shirin N-Power wani shiri ne da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa a ranar 8 ga watan Yunin 2016, domin magance matsalolin rashin aikin yi da matasa ke fama da su da kuma taimakawa wajen habaka ci gaban al’umma.

An dakatar da shirin na wani dan lokaci bayan da shugaba Bola Tinubu ya karbi ragamar mulki daga hannun Buhari, amma Edu ta bayyana cewa gwamnati mai ci tana son ta biya basukan da ake bi a baya kafin ta sake dawo da shirin.

“Har yanzu ba a sake kaddamar da shirin N-Power ba. Amma dai muna kokarin biyan basukan shekarun baya.

“Mun kasance muna da mai ba da shawara da ke kula da biyan wadannan kudade ga wadanda suka ci gajiyar N-Power. Duk da haka, an rike kudaden na tsawon watanni ba tare da biyan wadanda suka amfana ba.

“Don haka abin da gwamnati ta yi shi ne ta kwato kudaden ta kuma dawo da su asusun gwamnati kuma yanzu ta fara biyan wadanda ke cin gajiyar shirin don haka ne muke kira ga matasa da su yi hakuri.” Inji Ministan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here