Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 31 sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa kananan hukumomi 21 na jihar.
Kimanin mutane 280 ne bala’in ya shafa sannan gidaje 5,280 suka lalace.
Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, Isyaku Kubarachi ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba.
Hukumar ta ES ta ce, bala’in ya kuma kai ga lalata jimillar filayen noma 2,518, wanda ya mamaye kadada 976.
Kubarachi ya bayyana cewa ruwan sama mai karfi da ya haddasa ambaliya ya yi muni sosai inda mutane 135 suka samu raunuka yayin da wasu gidajen laka suka rufta a kansu.
Ya lissafa kananan hukumomin da abin ya shafa da suka hada da Wudil, Gwale, Nassarawa, Dala, Tarauni, Dawakin-Tofa, Dambatta da dai sauransu.
Sakataren zartaswar ya bayyana cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Yusuf ta dauki matakan da suka dace kafin damina don kare rayuka da dukiyoyi.