Gwamna Abba Kabir Yusuf, na jihar Kano ya bayyana kaduwarsa bisa wata gobara da ta yi sanadiyar mutuwar diya da kanwarta da kuma yayan kwamishinan ilimi mai zurfi, Dakta Yusuf Kofar Mata.
NAN ta rawaito cewa Yusuf ya jagoranci mambobin majalisar zartarwa na jihar da wasu manyan baki zuwa jana’izar wadanda suka rasu.
An gudanar da jana’izar ne a kofar Mata kwatas a ranar Laraba.
Yusuf ya bayyana wani abin takaici, lamarin da ya kai ga rasa rayukansu da ba su ji ba su gani ba tare da dukiyoyi masu yawa.
Karin labari: “Farashin saukan man fetur ya kai Naira 1,117 kowacce lita” – ‘Yan Kasuwa
“Cikin kaduwa mun samu labarin tashin gobara da ya yi sanadin rasa ‘yan uwan daya daga cikin mu guda uku.
“Wanda ya shafi kwamishinan ilimi mai zurfi, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata a gidansa da ke unguwar Kofar Mata a cikin birnin Kano.
“Hakika abin bakin ciki ne, mai ratsa zuciya, kuma abin takaici ne wanda zai dade a cikin zukatanmu.
“Muna mika sakon ta’aziyya ga kwamishinan da iyalansa baki daya, wadanda suka rasu kuma Allah ya gafarta musu, ya kuma kare afkuwar irin wannan munanan al’amura a gaba’’ in ji Gwamnan Kano, kamar yadda NAN ta tabbatar.