Kudin saukan man fetur ya kai Naira 1,117 kowacce lita a ranar Talata 16 ga watan Yuli, 2024, kamar yadda kungiyar Manyan Kasuwar Makamashi ta Najeriya ta sanar a ranar Laraba.
MEMAN ta bayyana hakan ne yayin wani taron yanar gizo da manema labarai a ranar Laraba.
Kungiyar ta bayyana cewa farashin man dizal ya kai Naira 1,157 a kowace lita, yayin da na man jiragen sama ya kai Naira 1,127.
Karin labari: “Ba’a kama Dan Zulum da kisan kai ba” – Gwamnatin Borno
A halin yanzu, gidajen mai da ke karkashin kamfanin NNPC da na manyan ‘yan kasuwa suna sayar da PMS a tsakanin N617/lita zuwa N660/lita, yayin da ‘yan kasuwa masu zaman kansu ke siyar da N700/lita ko fiye da haka.
Kamfanin mai na NNPC, wanda shi kadai ne ke shigo da man fetur a Najeriya, ya sha musanta batun bayar da tallafin kudin PMS amma ya ki bayyana kudin saukar da man.
Karin labari: Gobara ta kashe ‘yar Kwamishinan Kano, yayar sa da kuma matar dan uwansa
Sakataren zartarwa na MEMAN, Clement Isong, ya ce an samu kudaden ne daga masu samar da ma’auni masu zaman kansu na makamashi.
Kungiyar ta ci gaba da cewa za ta rika fitar da irin wadannan bayanai akai-akai domin fadakar da jama’a.
A kwanakin baya ne ‘yan kasuwar mai masu zaman kansu suka zargi masu gidajen man da masu zaman kansu da yin tsadar tsohon depot na man fetur daga naira 630 zuwa naira 720/lita.