Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Kano, Yusuf Kofar-Mata, ya rasa iyalansa uku a wata gobara da ta tashi a gidan sa.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a shafin sa na Facebook a ranar Laraba, inda yace wadan da suka mutu sun hada da babbar ‘yarsa ce mai suna Maimuna; yayarsa, Khadija, da matar yayansa, Juwairiyya.
An tattaro cewa gobara ta kone gidan kwamishinan da ke Kofar-Mata a Kano da safiyar Laraba yayin da iyalan ke barci.
Wata majiyar ta ce wutar ta lalata wasu kayayyaki masu darajar gaske a gidan.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Abdullahi Saminu, ya ce ba a iya gano irin barnar da gobarar ta yi da kuma musabbabin tashin gobarar ba.
Kofar-Mata ya bayyana alhininsa game da rashin da yayi.
“Ga Allah muka je, kuma gare shi za mu koma. Ina alhinin rashin ‘yata Maimuna (Islam) da yaya ta, Hajiya Khadija, da matar dan uwana, Juwairiyya, wadanda duk suka mutu a hadarin gobara da safiyar yau.
“Za a gudanar da Sallar Jana’izar su da karfe 11 na safe a Kofar-Mata kwatas, cikin birnin Kano a yau (Laraba),” in ji shi.