Dikko Radda ya mika ragamar jihar katsina ga Mataimakinsa

Dikko, Radda, mika, ragamar, jihar, katsina, Mataimakin
Gwamna, Dikko Radda, na jihar Katsina ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa Malam Faruq Lawal-Jobe a yunkurin tafiya hutu na wata daya. Gwamnan ya bayyana...

Gwamna, Dikko Radda, na jihar Katsina ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa Malam Faruq Lawal-Jobe a yunkurin tafiya hutu na wata daya.

Gwamnan ya bayyana haka ne a Katsina a wani taron hadin gwiwa da shugabannin kananan hukumomi da ‘yan majalisa da na zartaswa.

“Ina kuma so in yi amfani da wannan damar domin in sanar da ku cewa zan tafi hutu domin duba lafiya ta farawa daga ranar Alhamis har zuwa 18 ga watan Agusta.

Karin labari: Shehu Sani ya nuna damuwarsa kan matsalar tattalin arziki da rashin tsaro a Najeriya

“Don haka, na mika mulki a hukumance ga mataimakin gwamna don yin aiki a matsayin mukaddashin gwamna a wannan lokacin.

“Na kuma aike da takarda ga majalisa kuma sun amince min hutu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanada.

“Ina yi wa mukaddashin gwamna fatan alheri don sauke nauyin da ke kan ku. Kuma ‘yan majalisa da na shari’a da na majalisar zartarwa da shugabannin kananan hukumomi ina son ku ba shi hadin kai da goyon bayan da ya dace.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawan Najeriya ta cire Ndume daga mukamin mai tsawatarwar majalisar

“Ga al’ummar jihar Katsina, muna godiya matuka da kuka ba mu damar yi muku hidima,” in ji gwamnan.

A yayin taron, gwamnan ya kuma karbi karin kasafin kudin shekarar 2024 kamar yadda majalisar dokokin jihar ta zartar a ruwayar NAN.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here