Tinubu ya dage kan fara sabon tsarin haraji daga 1 ga Janairu duk da zargin sauya dokoki

Bola Tinubu Tinubu uk 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa sabbin dokokin haraji, ciki har da waɗanda suka fara aiki tun ranar 26 ga Yuni, 2025, da kuma sauran dokokin da aka tanadar za su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, za a aiwatar da su kamar yadda aka tsara tun farko.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar PDP ta sake kiran da a dakatar da ranar fara aiwatar da sabon Dokar Haraji, tana mai cewa akwai sabani tsakanin sigar dokar da Majalisar Tarayya ta amince da ita da kuma wadda daga baya aka wallafa a kundin dokoki, abin da jam’iyyar ta ce ya jawo babbar damuwa a faɗin ƙasar.

Shugaba Tinubu ya ce an lura da dukkan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar, amma ya ƙara da cewa babu wata matsala mai nauyi da aka tabbatar da ita da za ta sa a dakatar da tsarin gyaran harajin da ake aiwatarwa a ƙasar.

A cikin wata sanarwa, Tinubu ya jaddada cewa sabbin dokokin haraji ba wai an tsara su ne domin ƙara nauyin haraji a kan ‘yan ƙasa ba, sai dai domin sake gina tsarin tattalin kuɗi, daidaita dokoki, kare mutunci, da kuma ƙarfafa alaƙar gwamnati da al’umma.

Ya kuma yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su mara wa aiwatar da dokokin baya, yana mai cewa an shiga matakin aiwatarwa kai tsaye.

Karanta: Gwamnatin tarayya ba ta da ƙwarin gwiwar siyasa wajen shawo kan matsalolin tsaro — Kwankwaso

Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa tana sane da ce-ce-ku-ce da ake yi kan zargin sauya wasu tanade-tanade a cikin dokokin haraji da aka amince da su kwanan nan, amma ya jaddada cewa babu wata hujja mai ƙarfi da ta nuna an yi abin da ya dace a dakatar da fara aiwatar da dokokin.

Ya ƙara da cewa amincewa da doka a tsarin dimokuraɗiyya na buƙatar yanke shawara mai kyau a hankali, ba gaggawa ba.

Sai dai jam’iyyar PDP, ta bakin sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Ini Ememobong, ta bayyana cewa ‘yan Najeriya daga kowane fanni sun nuna bacin ransu kan abin da ta kira shigar da tanade-tanade masu hatsari cikin dokar haraji, duk da cewa Majalisar Tarayya ta cire su tun da farko.

Jam’iyyar ta ce hakan ya haifar da kira daga al’umma na a gudanar da cikakken bincike domin gano yadda aka shigar da waɗannan tanade-tanade.

PDP ta zargi fadar shugaban ƙasa da rage muhimmancin wannan batu, tana mai cewa gwamnatin tarayya ta fi bai wa batun kuɗi muhimmanci fiye da jin daɗin ‘yan Najeriya.

Jam’iyyar ta ce hakan ya nuna a fili inda fifikon gwamnatin Tinubu yake, tana kuma jaddada cewa shugaban ƙasa ya kamata ya tuna cewa shi ma’aikacin al’umma ne, kuma dole ne ya saurari ‘yan ƙasar, musamman ganin cewa bai samu fiye da kashi 40 cikin 100 na ƙuri’u a zaɓen da ya kai shi kan mulki ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here