Natasha Akpoti: ‘Yan mazabar Kogi ta tsakiya sun mika koke ga INEC don yi mata kiranye

Kogi Recall 750x430

Wata kungiyar masu rijistar zabe daga mazabar Kogi ta tsakiya sun mika takardar koke ga hukumar zabe ta kasa (INEC) a ranar Litinin inda suka nemi da ta gaggauta fara shirin dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan majalisar dattawa.

Al’ummar mazabar a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun jagoran masu shigar da kara, Salihu Habib, sun mika wa shelkwatar INEC da ke Abuja suna bayyana cewa yanzu ba su da kwarin gwiwa ga Akpoti-Uduaghan a matsayin sanata kuma wakiliyarsu a majalisar dokokin kasar.

Masu shigar da karar, a karkashin kungiyar Concerned Kogi Youth and Women, sun bukaci INEC da ta yi gaggawar yin aiki tare da nuna rashin son kai wajen gudanar da wannan bukata, domin tabbatar da dimokuradiyya, daidaiton shugabanci da zaman lafiya da ci gaban al’ummar Kogi da Nijeriya.

“Mu a matsayinmu na masu rajistar zabe na mazabar Kogi ta Tsakiya, muna neman ‘yancinmu a karkashin dokokin Tarayyar Najeriya domin muna bukatar a dawo da Sanata Akpoti-Uduaghan majalisar dattawan Najeriya a hukumance.

Karanta har ila yau: Ba lallai ba ne haɗakar ƴan siyasar Najeriya ta yi tasiri – Shekarau

“Musamman, wannan koke na kiran Akpoti-Uduaghan mun kawo shi ne bisa sashe na 69 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma ka’idoji na Hukumar INEC don duba korafe-korafe,” in ji masu shigar da kara.

A cewarsu, sama da rabin wadanda suka yi rajista a mazabar Kogi ta tsakiya ne suka sanya hannu kan takardar.

Da yake magana da manema labarai bayan gabatar da koken, jagoran mai shigar da kara ya bayyana kwarin gwiwar cewa tsarin zai kasance na farko da aka yi nasarar dawo da wanda aka dakatar a Najeriya.

Habib ya musanta zargin cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ne ya sanya su yin kiranyen.

Wata ‘yar kungiyar mai suna Misis Charity Omole ta bayyana cewa daukacin al’ummar mazabar Kogi ta tsakiya ba za su iya samun wakilci a majalisar dattawa na tsawon watanni shida masu zuwa ba.

“Don haka mun zo nan ne mu gaya wa INEC don Allah ta bi tsarin tsarin mulki domin a fara shirin kiran ta,” inji ta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here