Fasa gidan yari a Kogi: Hukumar NCoS ta kamo fursunoni 5 da suka tsere

NCos jail break 750x430

Hukumar kula da gidan yarin kasar nan (NCoS) ta sake samun nasarar cafke biyar daga cikin fursunoni 12 da suka tsere daga gidan yari a da ke Koton Karfe a jihar Kogi bayan da suka tsere.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Abubakar Umar, Jami’in hulda da jama’a na hukumar (SPRO), kuma mataimakin Kwanturola, (DCC), ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya tattaro cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 24 ga watan Maris.

NAN ta ruwaito cewa a lokacin da lamarin ya faru, wasu daga cikin ‘yan gidan yari na jiran shari’a (ATIs) a wani sashe na ginin kuma sun yi amfani da makullai wanda ya kai ga tserewar fursunoni 12.

Umar ya bayyana cewa da samun rahoton faruwar lamarin, mukaddashin shugaban hukumar ta NCoS, Sylvester Nwakuche tare da hadin gwiwar shugabannin hukumomin tsaro ‘yan uwa da suka hada da babban mai ba gwamnan Kogi shawara na musamman suka yi tattaki zuwa wurin.

Karanta: Natasha Akpoti: ‘Yan mazabar Kogi ta tsakiya sun mika koke ga INEC don yi mata kiranye

Ya ce an kuma tura jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya da farautar wadanda suka tsere.

“Ya zuwa yanzu, an sake kame biyar daga cikin fursunonin da suka gudu, yayin da ake ci gaba da damke sauran fursunonin da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.

“Muna kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu tare da ba jami’an tsaro hadin kai ta hanyar samar da duk wani bayani mai amfani da zai taimaka wajen kamo wadanda suka tsere”. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here