Atiku Abubakar ya musanta ficewa daga PDP

Atiku Abubakar, musanta, ficewa, PDP
Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da rahoton da ke cewa ya fice daga...

Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da rahoton da ke cewa ya fice daga jam’iyyar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi alkawarin ci gaba da marawa jam’iyyar ta PDP baya yayin da yake bayar da shawarar a gaggauta hadewar jam’iyyun adawa.

Karin labari: ‘Yan bindiga sun nemi diyyar triliyan 40

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, ya ce “Na sha kiraye-kirayen ‘yan jam’iyyarmu da magoya bayanmu, da kuma ‘yan Najeriya da suka damu, dangane da labarin da aka buga da ke nuna ficewata daga jam’iyyar PDP.”

“Wannan tsantsar karya ce. Ina kara jaddada biyayyata ga jam’iyyar PDP yayin da nake ba da shawarar a gaggauta hadewar jam’iyyun adawa” in ji Atiku Abubakar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here