Gwamna Radda ya dakatar da ma’aikatan cibiyar gyaran hali ta Katsina bisa zargin azabtar da fursuna

Dikko, Radda, mika, ragamar, jihar, katsina, Mataimakin
Gwamna, Dikko Radda, na jihar Katsina ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa Malam Faruq Lawal-Jobe a yunkurin tafiya hutu na wata daya. Gwamnan ya bayyana...

 

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya amince da dakatar da manyan jami’an Cibiyar Gyaran Hali ta Babbar Ruga bisa rahoton kwamitin bincike kan azabtar da wani fursuna, Usman Musa, wanda aka sare masa hannu daya, aka raunata ɗayan.

Wadanda aka dakatar sun haɗa da Shugaban cibiyar, Abdulzahir Abubakar; mataimakinsa, Bala Abubakar; da wani mai aikin ɗaki, Yunusa Yusuf.

Haka kuma an kori wani ma’aikacin wucin gadi, Murtala Suleiman.

Gwamnan ya bayar da Naira 970,000 don kula da lafiyar fursunan, tare da amincewa da Naira miliyan 35 domin samar masa da hannu na roba da ke da na’ura.

Ya kuma amince a gyara cibiyar domin dacewa da tsarin duniya na kula da fursunoni.

Kwamitin da Alhaji Usman Isiyaku ke jagoranta zai sa ido kan aiwatar da gyare-gyaren da aka amince da su.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here