Kashi 99% na masu garkuwa da mutane da aka kama a Anambra, Igbo ne, ba Fulani – Gwamnan jihar 

Soludo speaking at the town hall meeting with Anambra indigenes in the diaspora 750x430

Gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya ce kusan dukkan wadanda ake zargi da aikata laifuka da aka kama a jihar cikin shekaru uku da suka gabata ‘yan kabilar Igbo ne.

Soludo ya yi wannan tsokaci ne a yayin wani taro da ‘yan asalin jihar Anambra mazauna kasashen waje suka shirya, wanda aka gudanar a otal din Metro Points da ke New Carrollton, Maryland, Amurka.

Gwamnan ya ce tun da farko ya yarda da labarin cewa makiyaya ne ke haddasa tashe-tashen hankula da aikata laifuka a sassan Kudu maso Gabas.

“Na yi mulki tsawon shekaru uku da wata uku, idan muka kama masu laifi 100 da masu garkuwa da mutane, kashi 99.99% na matasan Igbo ne,” in ji gwamnan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here