Wasu ‘yan bindiga da suka kai sama da 200 sun kai farmaki a wasu kauyukan kananan hukumomin Kontagora, Mariga da Rijau a jihar Neja.
PRNigeria ta tattaro cewa ‘yan ta’addan sun afkawa al’ummomin ne a cikin ayarin kusan babura 100 tare da kashe yara a Bangi, wani yanki a karamar hukumar Mariga, inda suke rike da muggan makamai da alburusai, sun lalata gidaje da dama, tare da wawashe kayan abinci.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa PRNigeria cewa ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da shanu akalla 250 daga kauyukan da suka kai farmaki kan hanyoyinsu.
“Wadannan ‘yan ta’adda sun gudanar da ayyukan ta’addanci a cikin garuruwa da dama a yankin na Kontagora, Mariga da Rijau kamar yadda suka yi a baya.
“Baya ga korar al’ummar Argida, Babugadi, Warari, Birnin Boga, Mogola da wasu kauyuka, sun kuma kashe kananan yara a Bangi. Sauran mutanen kauyen kuma suka tsere.
“’Yan bindigar sun hau babura sama da 100. Sun yi nasarar yin awon gaba da shanu akalla 250, inda suka tafi dajin Maonda mai dimbin yawa,” in ji shi.
A halin da ake ciki, PRNigeria ta samu labarin cewa ‘yan sanda sun kaddamar da wani gagarumin aikin sa ido a dazuzzukan dake kananan hukumomin, domin yiwa ‘yan fashin kwanton bauna.
Wani ofishin leken asiri na soji, ya shaida wa PRNigeria cewa, rashin kyawun yanayi ne ya hana jiragen yakin sojojin saman Najeriya kai farmaki kan masu aikata laifuka.













































