Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC da kuma Ƙungiyar Ƙwadago ta Kasuwanci TUC sun sanar da shirin gudanar da gangamin goyon baya cikin lumana a ranar 3 ga Fabrairu domin nuna goyon baya ga Kwamitin Haɗin Gwiwar Ƙungiyoyin Ma’aikata JUAC.
Ƙungiyoyin sun bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da Babban Sakatare na NLC Benson Upah da kuma Sakatare Janar na TUC Nuhu Toro suka sanya wa hannu a Abuja.
Gangamin na da nufin tallafa wa yajin aikin ma’aikatan Hukumar Ci gaban Babban Birnin Tarayya FCDA da ke ƙarƙashin jagorancin JUAC, sakamakon rashin biyan albashi da suke fuskanta.
Ma’aikatan da ke ƙarƙashin JUAC sun fara yajin aikin ba tare da iyaka ba a 19 ga Janairu, lamarin da ya janyo rufe muhimman ofisoshin gudanarwa ciki har da Sakatariyar Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya FCTA da kuma FCDA.
An fara yajin aikin ne bayan cikar wa’adin gargaɗin kwanaki bakwai da aka bayar a ranar 7 ga Janairu, inda aka buƙaci shugabancin FCTA ya magance matsalolin da suka daɗe suna addabar ma’aikata kan walwala da haƙƙoƙinsu.
Ƙungiyoyin sun jaddada cewa gangamin zai nuna haɗin kai da tsayin daka na ƙwadago cewa cutar da ma’aikaci guda na nufin cutar da dukkan ma’aikata a cikin tafiyar ƙwadago ta Najeriya, tare da nuna adawa da duk wani nau’i na tsoratarwa ko zalunci a kan ma’aikata.
Sun ƙara da cewa gwagwarmayar ta JUAC halal ce kuma ba abin tattaunawa ba, kuma za a ci gaba da ita har sai an samu adalci, tare da umartar dukkan rassan ƙungiyoyi da majalisun jihohi su yi cikakken shiri da tura mambobinsu domin halartar gangamin.
Yayin da suka tabbatar wa ma’aikatan Babban Birnin Tarayya FCT cewa ba za a yi watsi da su ba.
NAN












































