Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philips Shaibu a ranar Asabar ya fice daga jam’iyy PDP zuwa APC.
Shaibu tare da wasu mambobin gamayyar jam’iyyar PDP ne ya sanar da sauya shekarsa a Benin a taron kaddamar da majalisar yakin neman zaben jam’iyyar na kasa a zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba.
Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa da sauran mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da suka tarbi mataimakin gwamnan, sun ce sun zo ne domin karawa jam’iyyar daraja.
Karin labari: ‘Yan sanda sun kama wasu mutane 3 da ake zargi da satar zinare a Abuja
A cewarsa, tabbas jam’iyyar adawa za ta karbe jihar bayan zaben gwamna.
Shi ma Shaibu ya samu karbuwa sosai daga Sanata Adams Oshiomhole, wanda mataimakin gwamnan ya kira mahaifinsa.
NAN, ta rawaito cewa an samu matsala ga Shaibu a jam’iyyar PDP lokacin da ya nuna sha’awar tsayawa takarar gwamna.
Karin labari: “Ambaliyar ruwa ya shafi wasu kananan hukumomi 3 a Kano” – SEMA
Burin dai ya sa mataimakin gwamnan ya kalubalanci shugaban sa, Gwamna Godwin Obaseki, wanda a karshe ya kai ga tsige mataimakin a ranar 18 ga watan Maris da majalisar dokokin jihar ta yi.
Sai dai wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da tsige shi a ranar Larabar da ta gabata, inda ta ce laifin da aka tsige shi bai kai na rashin da’a ba.