Osita Okechukwu, Darakta Janar, DG, na rediyon Muryar Najeriya, VON, ya ce Gwamnonin Jihohi ba za su iya ba wa kansu uzuri ba daga kasancewa manya-manyan ma su taimaka wa wajen kara ta’azzara talauci da rashin tsaro a Nijeriya.
Okechukwu ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja, yayin da ya ke mayar da martani kan matsayar kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, na cewa ya kamata a dora wa shugaban kasa Muhammadu Buhari laifin halin da kasar ke ciki.
“Ni ba mai magana da yawun gwamnatin tarayya ba ne ko kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sai dai kuma a matsayi na na mai goyon bayan Buhari, maganar gaskiya ita ce, ba ta inda gwamnoni za su wanke kan su wajen bayar da gudunmuwar abin da ha jefa ƙasar nan cikin talauci da rashin tsaro.
“Ba za su iya wanke kansu daga wannan ba,” in ji shi.
Okechukwu ya kara da cewa gwamnonin sun ɗora wa kansu wata izza ta mulki amma duk da haka ba zan su iya tsame kansu ba, bayan da su ka tattara kashi 47 cikin 100 na kudaden shiga na Majalisun Jihohi da Kananan Hukumomi, tare da kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke ba jihohi da kuma kudaden tallafi da su ka amsa.
“Wannan kuma ba a maganar ma irin dukiyar da su ka tara a haka,” in ji shi.
Ya ce ya kamata a tunatar da NGF cewa dukkanin hanyoyin tarayya, gadoji, madatsun ruwa, kiwon lafiya na matakin farko, shirye-shiryen ciyar da makarantu, shirin Anchor Borrowers Programme da dai sauransu duk suna a jihohi 36 na kasar nan.
Ya yi tambaya cewa ta yaya NGF za ta iya ba wa kanta uzuri alhali ta yi wa kananan hukumomi da ma’aikatun shari’a na Jiha da ‘yan majalisar dokoki kanshi mutuwa?
“Abin takaici, sakamakon shi ne tsananin talauci da rashin tsaro gaba daya. Ta hanyar yin almubazzaranci da kudaden kananan hukumomi, dakatar da bayar da kudade masu zaman kansu na bangaren shari’a da ‘yan majalisar dokoki na jihohi, NGF kara haifar da tabarbarewar tattalin arziki da kuma tada zaune tsaye, domin ana samun tsaro ta hanyar motsa jiki da dabarun farar hula,” inji shi













































