Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta bayyana shirin mayar da cibiyoyin zabe guda 16 a kananan hukumomi uku da ke fuskantar kalubalen tsaro a jihar Yobe.
Shugaban ayyuka na hukumar Alh Goni Usma ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki a Damaturu ranar Talata.
Usman ya ce za a kwashe cibiyoyin a kananan hukumomin Geidam, Yunusari da Gujba zuwa wuraren dake da cikakken tsaro.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa jami’in ya ce an mayar da kuri’u 1,109 zuwa rumfunan zabe, wanda ya kawo adadin rumfunan zabe a jihar zuwa 2,814.
A nasa jawabin, Shugaban sashin fasaha, Alhaji Lamido Ibrahim, ya ce adadin tsofaffi da sabbin katunan zabe guda 93,912 ne Hukumar ta tattara daga shekarar 2019 zuwa 2022.
Ya ce an raba guda dubu 49,399, yayin da adadin 44,513 suke a Hannun hukumar da ba a karba ba.
Ibrahim ya yi kira ga wadanda suka cancanci kada kuri’a wadanda ba su karbi katin zaben domin yin amfani da katin zabe.
Anasa Jawabin Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Haruna Garba, ya sake yin kira ga jam’iyyun siyasa da su mika tsarin yakin neman zabensu ga ‘yan sanda domin ba su kariya.













































