Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu a ranar Talata ya bayyana yadda ya tara dukiyar kudin sa.
Awata hira da gidan rediyon Birtaniya BBC ya bayyana yadda ya samu kudin sa, wanda ya yi ikirarin cewa ta hannayen jari ne, inda ya kara da cewa ba zai musanta iya adadin yawan dukiyar sa ba.
Tinubu wanda ya yi magana a kan batutuwa da dama, ya yi jawabi kan matsalar tsaro, ya kuma bayyana cewa har yanzu kasashen Yamma ba su ji dadin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba, dalilin kenan da ya sa suke kin sayar wa da gwamnatinsa makamai.
Sai dai ya ce ya yi imanin Buhari ya yi iya bakin kokarinsa a matsayinsa na shugaban kasa, don haka yayi iya kokarin sa wajan saisaita al’amuran kasar.
Tinubu, wanda ya ce yana da kwarin guiwa wajen kare irin nasarorin da Buhari ya samu a fannin tsaro, ya yi ikirarin cewa gwamnati mai ci, ta kawar da tashe-tashen hankula a kasar nan daga bala’in da suke fuskanta a baya.
Yayin da yake amsa tambaya kan yadda ‘yan Najeriya ke shan wahala a karkashin gwamnati mai ci, ya ce shi Bola Tinubu ne ba Buhari ba, don haka idan yayi nasara lamarin zai sha bamban.
Dan takarar na jam’iyyar APC ya bayyana akasarin wadanda ke tambayar tushen arzikinsa ko kuma yi masa tambayoyi a matsayin masu hassada.
“Na gaji dukiya mai tarin yawa kuma Ina jujjuyata ta hanyar kasuwanci iri daban daban,” in ji shi.
Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana cewa abin da zai sa a gaba shi ne tsaro da sake farfado da tattalin arzikin kasar tare da mai da hankali kan samar da ayyukan yi idan aka zabe shi.












































