Kotu ta bayar da belin mai sukar Ganduje, Muaz Magaji

30C1B23C AE02 4C57 82CA 7CA6C3EF1693
30C1B23C AE02 4C57 82CA 7CA6C3EF1693

Wata kotun majistare ta bayar da belin wani babban mai sukar gwamna Abdullahi Ganduje kuma tsohon kwamishinan ayyuka, Muaz Magaji a kan kudi Naira miliyan 1.

Kotun a ranar Juma’a, ta kuma umurci wanda ake kara a gaban shari’a kan wasu tuhume-tuhume guda hudu da ya bayar da mutum biyu da zasu tsaya masa, wanda daya daga cikinsu ya kasance mai unguwa a  kauyen Sarauniya, dayan kuma ya zama kwamandan Hisbah ko kuma babban limamin karamar hukumar Dawakin Tofa.

Alkalin kotun, Aminu Gabari ya dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 2 ga Maris, 2022 domin ci gaba da sauraron karar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here