Tono Man Fetur: Tawagar shugabanni a Gombe sun kaiwa Buhari Ziyarar Godiya

Gombe 2
Gombe 2

Tawagar shugabannin siyasa da na addini da ‘yan kasuwa daga jihar Gombe sun je fadar gwamnatin tarayya domin jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan rawar da ya taka wajen gano man fetur yankunan Kolmani.

Shugaban cikin raha yace: “Na gode da zuwan ku don ku yi mini godiya kan aikina. Na gode nakuma yaba da kokarin ku.”

Da ya ke tsikaci, Buhari ya ce lokacin da ya rike mukamin Ministan Man Fetur na sama da shekaru uku a shekarun 1970, “mun bullo da bincike, muna ganin kuma hakan zai kara daidaita siyasarmu.”

“Don haka, ya kamata ku taya kanku da kanku murna, kan kokarin da akayi na ganowa da neman man”

Buhari ya kuma ce ba tare da la’akari da abin da wasu ke cewa gwamnatin da ya jagoranta ta samu ci gaba wajen tabbatar da tsaro a kasar nan, farfado da tattalin arzikin kasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Buhari ya bayyana ziyarar a matsayin “karfafawa da kwarin gwiwa.”

Tunda farko a Jawaban sa, Jagoran tawagar Gwamna Inuwa Yahaya, ya ce mutanen Gombe sun zo ne domin nuna godiya bisa nasarar kaddamar da aikin mai na Kolmani.

Ya kara da cewa irin wannan gagarumin aikin wani muhimmin ci gaba ne ga daukacin kasar, “domin zai bunkasa tattalin arzikinmu, samar da ayyukan yi, da kuma amfanar manoma, ‘yan kasuwa, da kowa da kowa.”

A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Shehu Abubakar na lll, ya bayyana aikin Kolmani a matsayin abin tarihi, wanda mutane ba za su taba mantawa da su ba.

Ya yi alkawarin cewa ba za a samu rikici tsakanin jihohin Gombe da Bauchi ba, domin masarautar gargajiyar yankunan za ta zaburar da jama’a yadda ya kamata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here