‘Yan Bindiga Sun Kai Har Asibitin Abdulsalami Abubakar, Sun kashe Mutum 2 Tare da Sace Wasu

Nigeria Kidnappings Bandits deputy 1
Nigeria Kidnappings Bandits deputy 1

Wasu miyagu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai farmaki babban asibitin Abdulsalami Abubakar dake garin Gulu a karamar hukumar Lapai ta jihar Niger.

A yayin farmakin da ya auku a sa’o’in farko na ranar Talata, ‘yan bindigan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun halaka rayuka biyu kamar yadda Channels TV ta rahoto.

Channels TV ta tattaro cewa, mutane masu tarin yawa da suka hada da likitocin asibitin da masu bayar da magani suna cikin wadanda aka yi garkuwa dasu. Kamar yadda ganau ya bayyana, ‘yan bindigan sun bayyana da yawansu inda suka dinga harbi babu kakkautawa yayin da suke aiwatar da mugun nufinsu ba tare da wani kalubale daga jami’an tsaro ba ko ‘yan sa kai.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here