“Ambaliyar ruwa ya shafi wasu kananan hukumomi 3 a Kano” – SEMA

Ambaliya, ruwa, shafi, wasu, kananan, hukumomi, Kano, SEMA, NEMA, NiMet
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA, ta ce kawo yanzu akalla kananan hukumomi uku ne suka fuskanci ambaliyar ruwa a jihar. Sakataren zartarwa...

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA, ta ce kawo yanzu akalla kananan hukumomi uku ne suka fuskanci ambaliyar ruwa a jihar.

Sakataren zartarwa na SEMA, Alhaji Isyaku Abudullahi-Kubarachi, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Kano a wani taron masu ruwa da tsaki bayan wani atisayen kwaikwayo kan al’ummomin da ke cikin hadari.

Abdullahi-Kubarachi, wanda Daraktan tsare-tsare da bincike da kididdiga na hukumar, Umar Abdul-Aziz ya wakilta, ya lissafa kananan hukumomin da abin ya shafa da suka hada da Sumaila, Kibiya da Tudun Wada.

NAN, ya bayyana cewa Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi hasashen cewa kananan hukumomi 14 a jihar na daga cikin wadanda ke fama da matsalar ambaliya.

Karin labari: Majalisar wakilan Najeriya ta zauna da kamfanonin Siminti

Sauran kananan hukumomin sun hada da Rimin Gado, Tofa, Kabo, Madobi, Garun Malam, Bebeji, Rano, Dawakin Kudu, Warawa, Wudil, Sumaila, Ajingi, Kura da Dala.

Sakataren ya ce ya zuwa yanzu tawagar hukumar ta kai ziyara tare da tantance halin da ake ciki, inda daga nan ne za’a gabatar da cikakken rahoto na mikawa gwamnatin jihar domin samun kayayyakin agaji.

“Ba zan iya ba ku ainihin adadin mutane ko gidajen da abin ya shafa ba har sai bayan mun kammala rahotonmu,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa hukumar da masu ruwa da tsaki na duba yiwuwar samar da madatsar ruwa ta wucin gadi domin dakile illar da madatsar Tiga ke yi ga al’umma masu rauni.

Karin labari: Hukumar NAFDAC ta rufe wani gidan Burodi a Sakkwato

Sakataren ya yabawa asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) bisa tallafin da suke bayarwa wajen inganta iya aiki da taimakon kudi ta hanyar hadin gwiwa.

A nasa bangaren, kodinetan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) reshen jihar Kano, Dakta Nura Abdullahi, ya bayyana ingantaccen sarrafa shara a matsayin hanyar dakile ambaliya musamman a birane.

NAN ta rawaito cewa taron ya samu halartar wakilan SEMA na Jigawa, da Red Cross da Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) da dai sauransu jami’ai kamar yadda ta wallafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here