Hukumar NAFDAC ta rufe wani gidan Burodi a Sakkwato

NAFDAC, Hukumar, Sokoto, rufe, wani, gidan, Burodi
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta rufe wani gidan burodi saboda amfani da sikari da aka haramta amfani da shi a Sokoto....

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta rufe wani gidan burodi saboda amfani da sikari da aka haramta amfani da shi a Sokoto.

Ko’odinetan hukumar ta NAFDAC, Mista Garba Adamu, ya shaidawa NAN a ranar Juma’a cewa an gano gidan burodin ne a wani samame na musamman da jami’an hukumar suka kai.

“Wannan wata manufa ce ta Gwamnatin Tarayya da Hukumar NAFDAC da sauran hukumomin gwamnati ke aiwatarwa don tabbatar da cewa masu amfani da abinci sun samu mafi girman fa’idar abinci mai gina jiki da sauran fa’idojin kiwon lafiya daga kayayyakin da ake samarwa.

Karin labari: ‘Yan sanda a Katsina sun kama wani matashi kan zargin bada bayanai ga ‘yan fashi

“An kuma sanya wa wasu gidajen burodi shida takunkumi saboda rashin tsafta yayin da jami’an tsaro karkashin jagorancin Mista Buhari Manzo suka kara kaimi wajen kai ziyarar gani da ido a gidajen burodin da ke fadin jihar.

“Ana sa ido kan gidajen burodi don tabbatar da cewa ba sa amfani da saccharin ko wasu abubuwan da aka haramta a maimakon wasu kayayakin da aka sarrafa,” in ji Adamu.

Ko’odinetan ya ja kunnen masu sana’ar da su guji yin amfani da jabu ko marasa rajista da wa’adin aiki a wurarensu, inda ya kara da cewa NAFDAC za ta ci gaba da aiwatar da dokar a kowane lokaci.

Karin labari: Gwamnatin tarayya za ta bujuro da sabon tsarin makarantun Sakandire

Adamu ya ce za a fadada aikin ne zuwa kananan hukumomin a wani bangare na kokarin hukumar na ganin ana sayar da kayan abinci masu tsafta kamar yadda ya kamata.

Ya yi kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen ba da kayayyakin da ba’a yiwa rajista ba, kuma a ko da yaushe su kai rahoton duk wani abu da ake zargi da kuma gurbacewa ga hukumar ta NAFDAC, ya nanata ci gaba da kokarin hukumar na kare lafiyar al’umma kamar yadda NAN, ta tabbatar.

NAFDAC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here