Gwamnatin tarayya za ta bujuro da sabon tsarin makarantun Sakandire

Tahir, Mamman, Gwamnatin, tarayya, bude, sabon, tsarin, makarantun, Sakandire
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya ce a ranar Alhamis za a bullo da wani sabon tsarin karatu na makarantun sakandare a fadin kasar nan da watan Satumba...

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya ce a ranar Alhamis za a bullo da wani sabon tsarin karatu na makarantun sakandare a fadin kasar nan da watan Satumba na shekarar 2024.

Tahir ya bayyana haka ne a taron manufofin shigar da dalibai da na hukumar jarrabawar ta 2024 da ke gudana a Abuja.

“Muna aiki tukuru don ganin an bullo da sabon tsarin karatu na makarantun sakandire kafin watan Satumba,” in ji Mamman.

Karin labari: Gobara ta kashe ‘yar Kwamishinan Kano, yayar sa da kuma matar dan uwansa

Mamman ya bayyana cewa an gudanar da atisayen ne tun shekarar da ta gabata kuma za a gudanar da taron masu ruwa da tsaki a ranar 6 ga watan Agusta, 2024.

“Shirinmu ne cewa a watan Satumba, za a fara aiwatar da wannan shirin a dukkan makarantu, na gwamnati da masu zaman kansu,” in ji Ministan.

A kwanakin baya ne hukumar kula da manyan makarantun gaba da sakandire ta kasa ta yi Allah-wadai da halin da manyan makarantun kasar nan ke ciki tare da yin kira da a hada kai domin shawo kan wasu matsalolin da suka dabaibaye matakin karatun sakandire a kasar nan.

Karin labari: Gwamnan Kano ya jajantawa Kwamishinan Ilimi a sanadin gobara

Hukumar ta zayyana wasu daga cikin kalubalen da ke tunkarar wannan fanni da suka hada da nakasar ababen more rayuwa, da malaman da ba su cancanta ba, da tsofaffin manhajojin karatu, da dakunan karatu da dakunan gwaje-gwaje marasa kyau.

An kuma lura cewa ana ci gaba da shirye-shiryen bullo da wani sabon tsarin manhaja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here