Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin a dauki sama da malamai 4,000 aikin yi cikin gaggawa wadanda suke aiki karkashin shirin samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa (BESDA).
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Litinin.
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da rabon kayan koyarwa ga makarantu a Kano.
Ya bayyana cewa dukkan ma’aikata 4,000 za su yi gwajin kwarewa, kuma wadanda suka samu nasara za a ba su aikin dindindin a ma’aikatan gwamnati.
“Wannan wani bangare ne na kokarinmu na bayar da sakamakon sadaukar da kai da kuma tabbatar da samar da ingantaccen ilimi, kuma wadanda suka cancanta ne kawai za su shiga cikin tsarin,” in ji gwamnan.
Don haka Gwamnan ya ba da umarnin a tantance duk wanda ya nemi shiga aikin gwamnati cikin gaggawa a karkashin Hukumar kula da Ilimin bai daya ta Kasa (SUBEB).












































