PDP ta nada Ibrahim Shekarau a matsayin mamba a kwamitin Amintattu

Ibrahim Shekarau 750x430

Shugabancin jam’iyyar PDP ya nada Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, a matsayin mamba a kwamitin amintattun ta (BoT).

An tabbatar da nadin ne a wata takarda mai kwanan watan Mayu 9, 2025, mai dauke da sa hannun Sakataren BoT na PDP, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi.

“Ina so in sanar da kai cewa an zabe ka a matsayin mamba a kwamitin amintattu na babbar jam’iyyarmu, kamar yadda sashe na 32 (1) (a-h) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2017 ta bada dama,” in ji wasikar.

Karanta: Bukola Saraki zai jagoranci kwamitin sulhu na PDP

Wasikar ta kuma bayyana cewa wa’adin farko na Sanata Shekarau a matsayin mamban BoT shine na tsawon shekaru uku, daga ranar 12 ga Mayu, 2025, zuwa ranar 11 ga Mayu, 2028, kuma za’a iya sabunta shi na tsawon shekaru uku, kamar yadda sashe na 32(4) na kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

SolaceBase ta ruwaito cewa Sanata Shekarau ya taba rike mukamin Gwamnan Jihar Kano daga shekarar 2003 zuwa 2011 sannan kuma tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada shi Ministan Ilimi.

Ya kuma wakilci Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here