Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta kama wani yaro dan shekara 13, wanda ake zargin yana bayar da bayanai ga ‘yan fashi da makami.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Abubakar Sadiq-Aliyu ya bayyana hakan a Katsina.
“A ranar 3 ga watan Yuli, rundunar ‘yan sandan tare da hadin guiwar ‘yan kungiyar masu lura da al’amuran jihar Katsina (KSCWC) da ke kauyen Dansoda a karamar hukumar Dandume (LGA) sun yi nasarar cafke yaron mai shekaru 13.
“Yana zaune a unguwar Sheik Abdullahi da ke garin Dandume. An kama shi ne dangane da tuhumar da ake yi masa na taimakawa ‘yan fashi da makami.
Karin labari: Gwamnatin tarayya da Kungiyar Kwadago sun cemma matsaya kan sabon mafi karancin albashi
“An kama wanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri kan munanan ayyukansa. Ya kware wajen bayar da bayanai kan yiwuwar kai hari ga ‘yan bindiga da ake zargi.
“A yayin gudanar da bincike, ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, sannan kuma ya ambaci wani Abba, wanda a yanzu haka yake a matsayin wanda ya taimaka masa,” in ji Sadiq-Aliyu.
A cewarsa, wanda ake zargin ya kara da cewa yana cikin ’yan kungiyar da suka kai hari kauyen Unguwar Bawa sau da yawa, inda suka yi garkuwa da dabbobi da kuma sace su.
“Rundunar ‘yan sandan ta kuma yi nasarar cafke wani Musaddik Abdullahi da ke unguwar Kofar Kaura a Katsina, mamban wasu mutane hudu da suka yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.”
Karin labari: “Farashin saukan man fetur ya kai Naira 1,117 kowacce lita” – ‘Yan Kasuwa
Ya ci gaba da cewa, a wani gagarumin ci gaba da aka samu, jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar cafke wasu mutane uku da ake zargin ‘yan fashi da makami ne.
Ya ce wadanda ake zargin dukkansu mazauna kauyen Babbar Ruga ne da ke karamar hukumar Batagarawa ta jihar, an kama su ne bisa sahihan bayanan sirri kan ayyukansu.
Ya ce wadanda ake zargin sun kware wajen bayar da muhimman bayanai ga wani Mustafa Dan-Gambo, wanda ake zargin shugaban ‘yan fashi ne, wanda a halin yanzu yake hannun su.
“A yayin da ake gudanar da bincike, wadanda ake zargin sun amsa laifin da suka aikata. Ana ci gaba da gudanar da bincike” in ji kakakin ‘yan sandan, kamar yadda NAN ta tabbatar.