Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago sun amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris ne ya tabbatar haka ga manema labarai ranar Alhamis.
Ya ce gwamnati da shugabannin kungiyoyin sun cimma wannan matsaya ne bayan wata ganawa tsakanin shugaban kasa Bola Tinubu da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC a fadar gwamnati da ke Abuja.
Kafin taron na ranar Alhamis, Gwamnatin Tarayya ta yi tayin N62,000 a matsayin mafi karancin albashi yayin da kungiyar ta dage a kan N250,000 a matsayin albashin mafi karanci a Najeriya.
Bugu da kari, ministan ya bayyana cewa za a sake duba mafi karancin albashin zai kasance a duk bayan shekaru uku maimakon shekaru biyar a da.