Daya daga cikin gwamnonin jam’iyyar ya tabbatar da cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a mayar da Gwamna Mala Buni gefe a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa.
Gwamnan ya ce Shugaba Buhari, wanda wasu gwamnonin APC suka rinjaya, ba shi da wani zabi illa ya ba da umarnin tsige Buni sakamakon rikice-rikice da hargitsin da ba a gama ba a jam’iyyar da ke mulki gabanin gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa da za a yi a ranar 26 ga Maris.
Ana kuma zarginsa da shirya wata makarkashiya, tare da goyon bayan gwamnoni uku, domin kawo cikas ga babban taron da za a zabi sabbin shugabannin jam’iyyar.
‘Yan Najeriya da dama sun kadu matuka a lokacin da rahoton maye gurbin Mista Buni da wani gwamna ya fito a ranar Litinin.
A ranar Lahadi da daddare ne aka nada Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja, wanda kuma mamba ne a kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar, domin tafiyar da harkokin jam’iyya mai mulki.
A safiyar ranar Litinin ne Gwamna Abubakar Bello ya shiga sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja domin jagorantar taron kwamitin riko. Daga nan ne kuma ya rantsar da zababbun shugabannin jam’iyyar na jahohin da ke cike da cece-kuce.
Duk da dai ba a san ko menene manufarsa ba, PREMIUM TIMES ta lura da cewa gwamnan jihar Neja da isarsa sakatariyar ya ajiye motarsa a daidai inda aka kebe wa shugaban jam’iyyar na kasa.
Da yake yiwa ‘yan jarida jawabi gabanin ganawa da kwamitin shiyya na jam’iyyar APC, Bello bai fito fili ya yarda cewa an cire Buni ba sai dai kawai ya ce yana rike da mukamin shugaban kwamitin riko “tun” da gwamnan Yobe ya fita kasar waje neman lafiya.
“Na jima ina aiki tun lokacin da shugaban ya yi tafiya,” in ji shi, ya kara da cewa ya samu amincewar Mista Buhari.
A cewar majiyar mu, Mista Buni, wanda ke samun goyon bayan gwamnonin jam’iyyar uku, wato Yahaya Bello na jihar Kogi, da Hope Uzodinma na jihar Imo da kuma Dapo Abiodun na jihar Ogun, sun yi adawa da gudanar da babban taron kasa da ake sa ran za a yi.
Yayin da gwamnonin suka yi la’akari da furucin da shugaban kasa ya yi na sauya Shugabancin jam’iyyar don fara korar daya daga cikin abokan aikinsu, ‘yan kwamitin riko ne suka yanke hukunci na karshe, inda suka nada Mista Bello a matsayin wanda zai maye gurbin gwamnan Yobe.












































