Za’a rantsar da sabbin alkalan kotun koli guda 11

Kotun Koli
Kotun Koli

A watan Disambar 2023 da ta gabata ne Majalisar Dattawa ta tabbatar da alkalai 11 kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya bukata, za’a rantsar da sabbin Alkalan kotun kolin ne dai a mako mai zuwa da suka hada da:

Karanta wannan: KUST ta musanta karbar alawus na Naira Biliyan 1 daga Gwamnatin Kano

Hon. Justice Jummai Hannatu Sankey OFR Arewa ta tsakiya, da Hon. Justice Stephen Jonah Adah Arewa ta tsakiya, da Hon. Justice Mohammed Baba Idris, da Hon. Justice Haruna Simon Tsammani Arewa maso gabas, da Hon. Justice Jamilu Yammama Tukur na Arewa maso Yamma.

Karanta wannan: Katsina: An kashe Hakimi da ‘Dansa, tare da wasu mutane

Haka zalika akwai Hon. Justice Abubakar Sadiq Umar Arewa maso Yamma, da Hon. Justice Chidiebere Nwaoma Uwa Kudu maso Gabas, da Hon. Justice Chioma Egondu Nwosu-Iheme Kudu maso Gabas, da Hon. Justice Obande Festus Ogbuinya Kudu maso Gabas, tare da Hon. Justice Moore Aseimo A. Adumein Kudu kudu, da kuma Hon. Justice Habeeb Adewale O. Abiru na Kudu maso Yamma.

A na sa ran rantsar da su din dai, kotun koli za ta samu cikakkun alkalai 21, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanada.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here