Katsina: An kashe Hakimi da ‘Dansa, tare da wasu mutane

'Yan ta'adda
'Yan ta'adda

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Kukar Babangida da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina inda suka kashe hakimin kauyen Magaji Haruna da ‘Dansa.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa an kashe wasu mutane takwas a harin da aka fara da misalin karfe 10 na daren Laraba.

Karanta wannan: NITDA zata samar da cibiyar kere-kere ta zamani a Kano

“An kashe mutum 3 tare da wani a kauyen, Idris Haruna, a gida daya yayin da biyu kuma masu gadin wani kamfani ne. ‘Yan ta’addan sun yanka daya daga cikin masu gadin, sannan suka harbe dayan da bindiga.”
“Sun kuma kona manyan motoci biyu na kamfanin da wata mota guda daya,” in ji shi.

Wata majiya daga garin da ta tabbatar da labarin ta kuma kara da cewa an sace mata da ba’a tantance adadinsu a yayin harin ba.

Karanta wannan: Jami’ar Don ta gargadi Mata da su kaucewa shan miyagun kwayoyi

Ya yi zargin cewa an gano harin da aka shirya tun da misalin karfe 5 na yammacin Laraba lokacin da aka hangi ‘yan ta’addan suna taruwa a kauyukan Taka-Tsaba da Yargeza kuma an sanar da jami’an tsaro amma abin takaici ba’a yi wani abu da zai hana faruwar wannan mummunan lamari ba.

“Jami’an tsaro sun tabbatar mana da cewa akwai isassun jami’an tsaro da za su zo idan an kai hari, amma abin takaici ‘yan bindigar sun yi ta kai farmaki na sa’o’i da dama ba tare da wani kalubale ba. Motar aiki ce kawai ta zo bayan maharan sun tafi,” inji shi.

Mazauna yankin sun ce wasu jiga-jigan ‘yan fashi guda 2 suna gudanar da ayyukansu ne a karamar hukumar Jibia da kewaye.

Karanta wannan: Kano: Sakataren gwamnatin jiha ya dawo daga hutun jinya a kasar Saudiyya

Makwanni 2 da suka wuce, an kai wa wasu matafiya daga yankin Yangayya hari tare da kashe tara. Haka kuma lamarin ya faru ne a kusa da unguwar Kwana ukku, wanda bai kai kilomita biyu daga Kukar Babangida ba.

Wasu mazauna yankin sun nuna rashin jindadin su ga wadanda ke da alhakin gudanar da ayyukan kungiyar sa ido na al’umma da aka kafa a karamar hukumar.

Karanta wannan: Saudiyya: za mu iya daidaita alaƙa da Isra’ila amma bisa sharaɗi

Sun yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta binciki lamarin tare da yin abin da ya kamata don ceto yankin daga hare-haren ‘yan ta’addar.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutane tara ne kawai suka mutu, amma ya yi alkawarin karin bayani idan an kammala yin bincike.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here