Kano: Sakataren gwamnatin jiha ya dawo daga hutun jinya a kasar Saudiyya

IMG 20240110 WA0010 720x430
IMG 20240110 WA0010 720x430

Sakataren gwamnatin jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi, ya dawo gida daga hutun jinya a kasar Saudiyya, bayan shafe wata guda.

Tun a ranar 7 ga watan Disamba ne gwamnatin jihar Kano ta nada shugaban ma’aikata Abdullahi Musa a matsayin mukaddashin sakataren Gwamnatin kafin dawowar Dakta Baffa Bichi daga hutu jinya.

Karanta wannan: Gwamnan Jihar Kano ya nada sakataren gwamnati na wucin gadi

Matakin dai shi ne ya sanya aka fara maganganu kan gwamnatin Abba Kabir, da ta yi watanni bakwai da kafuwa.

Tun a wancan lokacin dai da ake ta maganganu, gwamnan ya fito ya bayyana cewa da zarar Dakta Baffa ya dawo daga jinya zai ci gaba da ayyukansa a matsayin Sakataren gwamnati.

Karanta wannan: Gwamnatin Kano za ta yi bincike akan gobarar Sakatariyar Gwale

Kazalika, ya bayyana karara cewa aikin Bichi yana nan yana jiransa, kuma yana so ya tabbatar da cewa har yanzu yana kan ragamar aiki.

Dawowar Baffan dai ta zo ne a daidai lokacin da rashin tabbas ya mamaye zukatan al’ummar jihar game da hukuncin da kotun koli zata yanke kan takaddamar kujerar gwamnan Kano.

Yayin dawowarsa da yammacin Talata, Dakta Bichi, ya samu tarba a filin jirgin sama na Aminu Kano daga ‘yan uwa da abokan arziki.

Karanta wannan: Gwamna Namadi ya jaddada aniyarsa ta bunkasa Ilimi da Lafiya a Jihar Jigawa

Sai dai ba a bayyana ko Baffan da ya dawo zai ci gaba da aikinsa nan take ne ko a’a ba.

Sai dai wata majiya ta shaida wa jaridar Solacebase cewa, Dakta Bichi, zai fara hutawa sannan ya tafi Abuja domin tarar da sauran jami’an da ke jiran hukuncin kotun koli.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here