Cutar kwalara ta kashe mutum 20 a Cross Rivers

320973401 1664646943953301 5244660386730318719 n
320973401 1664646943953301 5244660386730318719 n

A kalla mutane 20 sun rasa ransu yayin da wasu 30 kuma ke kwance a asibiti bayan da aka samu barkewar cutar kwalara a wasu kauyuka 10 da ke jihar Cross Rivers a kudancin Najeriya.

Mahukunta a jihar sun ce yawanci mutanen sun mutu ne a tsakanin ranakun 15 da 17 ga watan da Disambar shekarar da muke ciki.

Babbar jami’a a hukumar kulda da lafiya a matakin farko ta jihar, Janet Ekpeyong, ta shaida wa manema labarai cewa tuni gwamnatin jihar ta tura jami’an lafiya da kayan aiki zuwa yankunan da cutar ta barke don shawo kanta.

Ta ce, tawaga daga kungiyar likitoci ta Najeriya da wasu daga Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma na Kungiyar agaji ta Red Cross sun fara yunkuri don magance cutar a jihar.

Kauyukan da cutar ta barke na karkashin karamar Hukumar Abi, kuma suna fama da karancin tsaftataccen ruwan sha da kuma rashin tsaftar muhalli, abin da ake danganta wa da musabbabin barkewar cutar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here