Cikin Hotuna: Buhari ya kaddamar da rukunin gidajen malaman Makaranta da Zulum ya gina musu

Borno teachers estate 1 1 750x430 1
Borno teachers estate 1 1 750x430 1

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da sabon rukunin gudajen malamai da Gwamna Babagana Umara Zulum ya gina, a Jihar Borno.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa rukunin gudajen, wanda yana daya daga cikin manyan ayyuka sama da 600 da Zulum ya gabatar, an yi shi ne a Bulumkutu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ya fitar a ranar Alhamis, ta ce rukunin gidajen malaman suna dauke da dakunan kwana biyu an kuma zagaye su.

Sanarwar ta ce, tun da misalin karfe 12 na rana Buhari ya isa rukunin gidajen malaman tare da Gwamna Zulum da mataimakin gwamnan Umar Usman Kadafur da Dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima da wasu ‘yan majalisar tarayya daga jihar Borno da ministar harkokin jin kai, da kare ibtila’i Sadiya Umar Farouq, da Manajan Darakta na Hukumar Raya Arewa maso Gabas, da manyan jami’an gwamnati.

‘’ Ana sa ran Buhari zai kaddamar da rabon abinci na musamman ga iyalan wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, yayin da kuma zai kaddamar da matsugunnai 500 ga ‘yan gudun hijirar da gwamnatin tarayya ta gina a Molai da ke wajen birnin Maiduguri.

up
‘’Gidajen na cikin gidaje dubu 10,000 da shugaba Buhari ya amince da su a shekarar 2021, inda kawo yanzu tuni an kammala sama da gidaje dubu 6,000. ”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here