Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya nesanta kansa daga wani shirin taimako da ake kira “Atiku Grant by FG” da ake ta yayatawa a kafafen sada zumunta, yana cewa zamba ce don yaudarar mutane.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa, Paul Ibe, ya fitar, Atiku ya bayyana cewa babu wani shiri na taimako da yake gudanarwa ko wata kungiya da ke da alaka da shi da ke bayar da N65,000 ga masu nema.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki wadanda ke tallata wannan shiri da sauran makamantansa, sannan su dauki matakin da ya dace don kare ‘yan kasa daga fadawa tarkon zamba.