Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya mika sunayen mutane 6 ga majalisar dokokin jihar a matsayin kwamishinoni.
Kakakin majalisar, Ismail Jibrin Falgore ne ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin da yake karanta wasikar gwamnan a zauren majalisar.
SolaceBase ta rahoto cewa wadanda aka nada sun hada da, Shehu wada Sagagi, Dr Dahiru Mohd Hashim, Ibrahim Abdullahi Wayya, Dr Isma’il Dan Maraya, Gaddafi Sani Shehu da Abdulkadir AbdulSalam.