Harin Jos: Atiku ya soki Tinubu kan ziyarar jaje da ya kai a iya filin jirgi a Plateau

former Vice President Atiku Abubakar 750x430

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya soki ziyarar ta’aziyyar da Shugaba Bola Tinubu ya kai jihar Plateau, yana mai bayyana hakan a matsayin alamar rashin fahimtar halin da talakawa ke ciki.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa Phrank Shaibu ya fitar a Abuja, Atiku ya nuna damuwa kan yadda shugaban kasa ya mayar da martani ga kashe-kashen da suka faru a wasu sassan Plateau, yana mai cewa ziyarar ba ta kai matsayin tausayi da gaggawar da ake bukata ba.

Ya bayyana cewa abubuwan da suka faru a Plateau sun sake bayyana wata hanya mai tayar da hankali da ba za a amince da ita ba wajen magance bala’o’in kasa.

Ya ce abin mamaki ne yadda bayan kwanaki da kashe-kashen fararen hula, abin da aka kira duba halin da ake ciki ya tsaya ne kawai a bakin jirgi, ba tare da isa wuraren da abin ya shafa ko tuntubar wadanda ke cikin jimami ba.

Ya kuma kara da cewa abin da ya fi damuwa shi ne yadda aka takaita ziyarar domin shugaban ya wuce zuwa Lagos don hutun Easter, yana mai cewa hakan na nuna rashin dacewar fifikon da aka bai wa abubuwa a lokacin da kasa ke cikin jimami.

Atiku ya zargi shugaban da mayar da ziyarar da ya kamata ta kasance ta tausayi zuwa wani lamari na siyasa, inda ya gana da ‘yan jam’iyyarsa a Jos maimakon kai ziyara ga wadanda abin ya shafa.

Ya ce yadda aka gudanar da ziyarar Plateau na nuna irin yadda ake mayar da martani ga bala’o’in kasa ta hanyar da ke cike da siyasa maimakon nuna kulawa.
Ya kuma ambaci irin wata ziyara makamanciya da aka kai jihar Benue a shekarar 2025, yana mai cewa hakan na nuna cewa wannan dabi’a ce da ake maimaitawa ba kuskure guda daya ba.

Ya ce shugaban bai ziyarci iyalan wadanda suka rasu ko wadanda ke jinya a asibiti ba, kuma bai bayar da wata cikakkiyar hanya ta magance matsalar tsaro ko tabbacin cewa irin wannan lamari ba zai sake faruwa ba.

Ya kara da cewa maimakon haka shugaban ya gudanar da wata ganawa a cikin filin jirgi tare da ‘yan siyasa da sarakuna, lamarin da ya yi nesa da halin kuncin da jama’a ke ciki.

Kalaman Atiku sun zo ne bayan shugaba Tinubu ya kai ziyara jihar Plateau sakamakon hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 27 a Jos, musamman a yankin Angwan Rukuba.

A yayin ziyarar, shugaban ya gana da wata uwa da ta yi fice a bidiyo tana rungume da gawar danta, inda ya tausaya mata tare da yi wa iyalan wadanda abin ya shafa alkawarin tallafi daga gwamnati.

An tarbi shugaban a Jos ne daga shugaban APC na kasa Nentawe Yilwatda, gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang da sauran manyan jami’an gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here