Karin kudin sadarwa zai kayo cikas ga tsarin koyo da koyarwa – Dalibai sun koka

telecom new 750x430

Dalibai a jihar Enugu, a ranar Laraba,  sun yi kira da a duba batun karin harajin kashi 50 cikin 100 na sadarwa saboda matsalar tattalin arziki da ake fama da ita.

Suna ce ayyukan sadarwa, kamar sabis na intanet, sun inganta aikin koyo da bincike; kara harajin sadarwa zai kawo cikas ga tsarin binciki, koyo da koyarwa.

Sun bayyana hakan ne ya yin zantawar su da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

Mista Divine Eze, dalibin dake karantar tsarin kula da Muhalli a Jami’ar Najeriya Enugu Campus (UNEC), ya bukaci Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) da kamfanonin sadarwa da su janye batun karin harajin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here