‘Yan Sanda Sun Ceto Matar Tsohon Mataimakin Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Mai Ritaya, Sun Kwato Kudin Fansa

Hakeem Odumosu

Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun ceto Folashade Odumosu, matar tsohon mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Hakeem Odumosu.

A ranar Laraba ne matar da aka I garkuwa da ita ta sami ‘yancinta.

An tattaro cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Lanre Ogunlowo ne ya jagoranci aikin ceto matar AIG mai ritaya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi, ya tabbatar da hakan a shafin sa na X a safiyar ranar Alhamis

A yayin aikin, an kashe masu garkuwa da mutane.
Adejobi ya ce jami’an sun kwato kudin fansa da aka biya masu garkuwa da mutanen.

Sai dai ya ki bayyana adadin kudin da aka biya ga masu garkuwa da mutane ko kuma ainahin inda aka ceto wanda akai garkuwa da itan.

Adejobi ya ce, Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya yabawa CP da jami’an ‘yan sanda bisa kokarin ceto su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here