Kungiyar Kwankwasiyya ta bukaci shugaban INEC ya yi murabus, ta kuma nemi dakatar da tantance masu kada kuri’a

INEC Chairman Joash Amupitan

Kungiyar Kwankwasiyya ta nuna matukar damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin barazanar da ke kara karfi ga dimokuradiyyar Najeriya, tana mai danganta hakan da sabanin hukuncin kotuna da kuma yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ke gudanar da ayyukanta.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed ya fitar, ya bayyana cewa rikicin shugabanci da ke cikin jam’iyyar ADC da kuma matakin da INEC ta dauka na dakatar da amincewa da kowanne bangare har sai kotu ta yanke hukunci, na nuna yadda cibiyoyin dimokuradiyya ke cikin wani hali mai rauni.

Kungiyar ta bayyana cewa sabanin hukuncin kotuna da kuma wasu matakan gudanarwa da hukumar zabe ke dauka na raunana jam’iyyun adawa tare da kawo cikas ga tsarin siyasa.

Ta kuma lura cewa irin wadannan rikice-rikice sun shafi manyan jam’iyyun siyasa da dama ciki har da PDP da LP da NNPP.

A cewar sanarwar, wadannan matsaloli da ke maimaituwa, wadanda akasari ke samo asali daga sabanin hukuncin kotuna, sun haifar da tsawon rikice-rikicen shugabanci tare da raunana dimokuradiyyar cikin gida a jam’iyyun siyasa.

Kungiyar ta kara nuna damuwa kan abin da ta kira rashin bin ka’idojin doka, musamman yadda kotuna masu matsayi iri daya ke yanke hukunci masu karo da juna.

Ta yi gargadin cewa irin wannan hali na iya lalata martabar bangaren shari’a tare da bude kofar yin anfani da tsarin zabe ba bisa ka’ida ba.

Har ila yau, kungiyar ta soki shirin da INEC ke yi na sake tantance masu kada kuri’a gabanin zabuka masu zuwa, tana mai cewa lokacin da aka zaba bai dace ba kuma zai iya hana wasu ‘yan kasa hakkinsu na kada kuri’a.

Kungiyar ta ce wannan tsari na iya rage yawan masu kada kuri’a tare da shafar wasu bangarori na al’umma fiye da wasu.

Ta yi gargadin cewa haduwar wadannan matsaloli na sabanin hukuncin kotuna, rikice-rikicen jam’iyyun siyasa da kuma damuwar da ke tattare da harkokin zabe, na iya zama babbar barazana ga sahihancin zabuka masu zuwa musamman yayin da Najeriya ke shirin zaben 2027.

Saboda haka, kungiyar Kwankwasiyya ta bukaci shugaban INEC ya yi murabus nan take, a dakatar da shirin tantance masu kada kuri’a, sannan ta nemi Majalisar Shari’a ta Kasa NJC ta dauki matakin gaggawa domin magance sabanin hukuncin kotuna.

Kungiyar ta kuma bukaci ‘yan siyasa da su guji amfani da bangaren shari’a don cimma muradunsu na siyasa, tare da kira ga kungiyoyin fararen hula da kasashen duniya su sanya ido domin kare dimokuradiyyar Najeriya.

Ta kara da cewa makomar Najeriya na dogara ne da karfin cibiyoyi, sahihancin tsari da kuma kare hakkin ‘yan kasa na zabar shugabanninsu cikin ‘yanci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here